Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta sanar da cewa mayakan gwagwarmaya sun yi wa wani sabon wurin da sojojin Isra'ila suka kafa don gudanar da umarnin yaƙi a garin "Al-Bayada" ruwan bam da jirgin sama mara matuki a yau Litinin, kuma bama-baman sun kai hari kai tsaye kan wurin da aka kai harin. Sannan Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta harba makamai masu linzami kan taron sojojin Isra'ila a garin Al-Qantara.
Hizbullahi ta kai hari kan matattarar sojojin Isra'ila da sabon sansanin kai hare-hare a kudancin Labanon
Your Comment